Abba Gida-Gida Ya Dawo Da Muhuyi Magaji Shugabancin Hukumar Yaƙi Da Cin Hanci Ta Jihar Kano

Gwamnatin jihar Kano, ta dawo da Muhuyi Magaji Rimin Gado kan muƙaminsa na shugaban hukumar karɓar korafe-korafe da kuma yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano.

A wata sanarwa mai ɗauke da sahannun mai magana da yawun gwamnan jihar Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya ce an dawo da Muhuyi ne domin ya kammala wa’adin mulkinsa kamar yadda hukunci ya ce.

Bature ya ce dawowar ta fara aiki ne nan take.

Gwamnatin, tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje ce ta sauke shi daga muƙaminsa.

Muhuyi ya garzaya kotu inda ya kalubalanci matakin na gwamnati.

More from this stream

Recomended