A shirye nake na biya mafi ƙarancin albashi na ₦70,000 a cewar gwamnan Kebbi

Gwamna Nasiru Idris na jihar Kebbi ya ce gwamnatinsa a shirye take ta biya ma’aikatan jihar Kebbi mafi ƙarancin albashi na ₦70,000.

Gwamnangg ya bayyana haka a birnin Kebbi ranar Juma’a lokacin da shugabannin kungiyar ƙwadago ta NLC na jihar suka kai masa ziyara a ofishinsa.

Ya ce wasu mutane suna zagawa suna faɗin cewa gwamnatin jihar baza ta biya mafi ƙarancin albashi ba.

Gwamnan ya yiwa ma’aikatan alƙawarin zai hanzarta aiwatar da fara biya mafi ƙarancin albashin da zarar an miƙawa gwamnatin jadawalin tsarin yadda ƙarin zai kasance.

Ya ƙara da cewa ita kanta gwamnatin tarayya da ta amince da ƙarin albashi bata fara biya ba ya cigaba da cewa da zarar gwamnatin ta shirya to za su zauna da ƴan kungiyar ƙwadagon domin fitar da hanyar da ta dace aiwatar da ƙarin.

More from this stream

Recomended