A lura sosai game da yadda jabun takardun naira suka yawaita—CBN ya gargadi ƴan Najeriya

Babban bankin Najeriya, CBN, ya gargadi ‘yan Najeriya da su yi hattara da kudaden Naira na bogi da ke yawo ba bisa ka’ida ba.

Wannan gargadi na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mukaddashin daraktan sadarwa na CBN, Hakama Sidi Ali, ta fitar a Abuja ranar Juma’a.

“An jawo hankalin Babban Bankin na CBN a kan yadda ake yada takardun kudi na jabu, musamman manyan kuɗaɗen da wasu mutane ke yi,” in ji ta.

Sidi Ali ya te jabun na Naira an fi amfani da shi wajen hada-hadar kasuwanci a kasuwannin abinci da sauran cibiyoyin kasuwanci a fadin manyan kasuwanni a garuruwan kasar.

Ta ce duk wanda aka samu da hannu wajen shigar da kudaden na jabu to zai fuskanci hukunci mai tsanani.

Draktar ta ce dokar ta tanadi hukuncin zaman gidan yari wanda ba zai yi kasa da shekaru biyar ba, ga duk wanda aka samu da laifin yin jabun kudin Naira ko kuma duk wata takardar doka a Najeriya.

“CBN na ci gaba da hadin gwiwa da hukumomin tsaro da wadanda suka dace domin kwato takardun kudin Naira na bogi, kamawa da hukunta masu yin jabun.”

“Ana kuma kara kira ga jama’a da su kai rahoton duk wanda ake zargin yana da kudin jabun naira ga ofishin ‘yan sanda mafi kusa, reshen CBN, ko ta contactcbn@cbn.gov.ng,” in ji ta.

More News

An ƙona sakatariyar ƙananan hukumomi 2 a jihar Rivers

Wasu da ake kyautata zaton ɓatagari ne sun ƙona wani sashe na sakatariyar ƙananan hukumomin Eleme da Ikwerre dake jihar Rivers. Ƙona ginin na zuwa...

Ƴansanda sun hallaka masu garkuwa da mutane

Ƴansanda sun hallaka wasu masu garkuwa da mutane uku da ake zargin sun yi yunkurin yin garkuwa da matar wani dan majalisar dokokin jihar...

Ƴanbindiga sun hallaka wani shugaban APC a Kebbi

Wasu ‘yan bindiga sun harbe Bako Bala, shugaban jam’iyyar APC na karamar hukumar Suru a jihar Kebbi, a yayin wani yunkurin yin garkuwa da...

Kotu ta hana VIO kamawa, tsare motoci ko cin tarar direbobi a kan hanya

Justis Evelyn Maha ta Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta bayar da umarni da ya hana Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa, wanda aka...