
Rundunar ƴansandan Najeriya ta ce tana da cikakken izinin kotu da ya bata damar kama Sanata Dino Melaye a gidansa dake Abuja.
Idan za a iya tunawa jami’an ƴansandan sun yiwa gidan sanatan kawanya domin kama shi bisa zargin hannu da yake da shi a aikata kisan kai.
Melaye sanata mai wakiltar mazabar Kogi ta yamma tare da wasu mutane ana zarginsu da kisan wani jamin ɗansanda mai suna Sajan Danjuma Saliu dake aiki da rundunar ƴansandan kwantar da tarzoma ta 37 lokacin da yake bakin aiki a Aiyetoro Gbede kan titin Mopa dake jihar ta Kogi.
A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ƴansanda ta kasa, Jimoh Moshood ya fitar ranar Litinin a Abuja ta ce ƴansanda za su cigaba da kasancewa a gidan har sai ya mika wuya.
“Baza mu ja da baya ba har sai Sanata Dino Melaye ya mika kansa an kama shi domin bincike.”