
Gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari Abubakar ya ziyarci sojojin da suka jikkata a wani harin kwanton bauna da barayi suka kai musu a jihar.
Yanzu haka sojojin na cigaba da murmurewa a Cibiyar Kula Da Lafiya Ta Tarayya dake Gusau.
Gwamnan ya samu rakiyar,Sunusi Rikiji shugaban majalisar dokokin jihar da kuma sauran shugabannin hukumomin tsaro dake jihar.
A wata sanarwa da Ibrahim Dosara mai magana da yawun gwamnan ya fitar ya bayyana cewa gwamnan da tawagarsa sun samu tarba daga Kaftin Ahmad Danjuma.
Yayin ziyarar Gwamna Yari ya bayyana farin cikinsa kan yadda sojojin suke samun sauki.
Wasu yan bindiga ne suka budewa motar sojojin wuta har ta kai s
Matsalar rashin tsaro a jihar ta Zamfara abune da ya zama abin damuwa a wurin gwamnati.