
Mayakan kungiyar Boko Haram da suka kai hari kan garin Buni Gari dake jihar Yobe sun gamu da gamon su lokacin da suka gwabza fada da wasu mafarauta ranar Lahadi.
Wani mazaunin garin wanda ya fadawa jaridar The Cable haka ya ce mayakan na Boko Haram sun kai harin ne da misalin karfe 5:00 na yamma.
Ya ce duk da cewa babu sojoji a garin lokacin da suka kawo harin mafarautan sun tilastawa yan ta’addar ja da baya.
Wata majiyar ta kara da cewa duk da cewa an kori mayakan mutane sun gudu daga garin.
“Mutane da dama sun gudu ya zuwa garin Buni Yadi dake kusa saboda fargabar da suke yi mayakan Boko Haram za su iya tattaruwa su kawo mummunan hari,”ya ce.
“Buni Yadi tafi tsaro fiye da Buni Gari saboda akwai sojoji a can.”
Mayakan Boko Haram sun kara zafafa hare-hare a yan kwanakin nan musamman a jihohin Yobe da Borno.