Majalisar dokokin jihar Adamawa ta shiga cikin rikici

Rikici na cigaba da ƙamari a majalisar dokokin jihar Adamawa bayan da aka tsige mataimakin shugaban majalisar, shugaban masu rinjaye da kuma wasu shugabannin majalisar biyu.

Rikicin ya fara ne a ranar Asabar bayan zaman majalisar da mataimakin shugaban majalisar, Emmanuel Tsamdu ya jagoranta ya amince da zartar da kasafin kudin shekarar 2019.

Mamba mai wakiltar mazabar Mubi North,Sani Shehu shine ya gabatar da sahannun wakilai 17 dake neman a tsige Tsamdu.

Sauran mambobin da aka cire sun hada da shugaban masu rinjaye,Hassan Barguma,mataimakin shugaban masu rinjaye, Abubakar Isa da kuma mataimakin bulaliyar majalisar Abdullahi Nkepeyi bisa dogaro da rashin kwarin gwiwa da suke da shi kan shugabancinsu.

Tsamdu ya dage kan cewa mambobi 17 da suka rattaba hannu kan takardar tsige shi basu halarci zaman majalisar ba saboda haka dole ne su bayyana domin tabbatar da sahannun nasu.

Shima Burguma wanda ya dage kan cewa har yanzu shine shugaban masu rinjaye ya fadawa jaridar Daily Trust cewa akwai yunkurin da ya gaza yin nasara da wasu 14 daga cikin yan majalisar 25 suka yi na cire Tsamdu da kuma wasu shugabannin majalisar.

Rikicin shugabanci wani abu ne da ya zama ruwan dare a majalisun dokokin jihohin Najeriya.

Masana da dama na alakanta haka kan tsoma baki da gwamnoni jihohi kanyi wajen gudanar da majalisun.

A yanzu dai shugaban kasa Muhammad Buhari ya sanya hannu kan wata doka da ta bawa majalisun jihohi yan cin gashin kai ta bangaren kudade.

More from this stream

Recomended