Mayakan Boko Haram sun sake kai hari a wani kauye dake jihar Borno

Wasu al’ummomi dake karakashin karamar hukumar Monguno ta jihar Borno sun fuskanci hare -hare daga mayakan kungiyar Boko Haram a daren jiya.

Wani mazaunin yankin ya fadawa jaridar The Cable cewa mayakan Boko Haram sun farma kauyen Kekeno daya daga cikin kauyukan da abin ya shafa da misalin karfe 06:00 na yamma inda suka shiga musayar wuta da sojoji.

Ya ce maharan sunje cikin shiri dauke da makamai inda ya kara da cewa an dauki tsawon sa’o’i biyu ana dauki ba dadi tsakanin su da sojoji.

“Yan ta’addar sun zo cikin shiri suna bindigogin kakkabo jiragen sama iri daban-daban da suka kafa a wurare daban-daban,”ya cce.

Ya zuwa yanzu dai babu cikakken bayani wane bangaren kungiyar Boko Haram ne yake da alhakin kai harin.

More from this stream

Recomended