
Ministan harkokin cikin gida, Abdulrahman Bello Dambazau ya ce za a kara tura karin jami’an tsaro jihar Zamfara domin kawo karshen kashe-kashen da kuma lalata dukiya da ake .
Dambazau ya bayyana haka ne lokacin da ya ziyarci jihar a ranar Alhamis.
Ministan ya samu tarba daga mai rikon muƙamin gwamnan jihar, Sunusi Rikiji da kuma sauran yan majalisar zartarwar jihar.
Ya yin ziyarar ministan ya bayyana damuwar shugaban kasa Muhammad Buhari kan halayyar kin tuba da masu aikata kashe-kashe a jihar suke da ita.
“Mun himmatu wajen aiki tare da gwamnatin jiha wajen kara tura jami’an tsaro zuwa jihar,”
A ranar Laraba ne dai ministan ya bayyana cewa rikicin na Zamfara na zai iya kawo karancin abinci a kasarnan.