Gwamnan jihar Nassarawa a arewacin Najeriya ya bayar da shawarar cewa a bar kowace jiha ta tantance karancin albashi da za ta iya biyan ma’aikatanta.
An dade ana kiki-kaka kan albashi mafi karanci da gwamnatoci da kamfanoni za su biya ma’aikata a kasar ta Najeriya.
Bayan tattaunawa da kungiyar kwadago gwamnatin tarayyar kasar na ganin cewa Naira dubu 30 (Kimanin Dala 83) ne abinda ya dace a biya a matsayin karancin albashi.
Sai dai gwamnonin jihohi sun ce ba za su iya biyan hakan ba.
Gwamnan jihar Nassarawa, Umar Tanko Almakura ya ce a lokacin da wasu jihohin za su iya biyan sama da dubu 30 a matsayin karancin albashi ga ma’aikata, akwai jihohi wadanda a yanzu da kyar suke iya biyan Naira dubu 18, wato kimanin Dalar Amurka 50, wanda shi ne karancin albashin ma’aikata da ake amfani da shi a kasar.
Ya ce “Idan ka duba kudin da za a biya(Idan aka kara albashi), da kuma halin da ake ciki, jihohi da dama za su samu matsala sosai wurin biyan wannan kudi”.
Gwamnan ya kuma ce za a samu matsala idan aka ce kananan jihohi su biya ma’aikata albashi daidai da na jihohi masu karfin tattalin arziki.