Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane 15 a jihar Niger

Wasu yan bindiga a ranar Talata sun yi garkuwa da mutane 15 tare da kashe wasu biyu a garin Mangwaro dake kan iyakar jihohin Kaduna da Niger.

Jaridar Daily Trust ta gano cewa an yi garkuwa da mutanen ne akan hanyarsu ta dawowa daga Kaduna.

Danjuma Sallau kwamishinan yada labarai na jihar Niger wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Laraba ya bayyana cewa 10 daga cikin mutanen sun fito ne daga garin Gwada na karamar hukumar Shiroro ta jihar ya yin da ragowar mutanen suka fito daga karamar hukuma Munya.

Akwai dai zaman d’ar-d’ar a kananan hukumomin,Munya,Rafi da Shiroro dake jihar bayan da ake zargin samun kwararar yan bindiga dake guduwa daga jihar Zamfara.

Sallau ya bayyana cewa ya ziyarci Sarkin Pawa hedkwatar karamar hukumar Munya kuma tuni aka tattara wata tawagar jami’an tsaro da suka hada da sojoji, ƴansanda, jami’an Civil Defence da kuma yan bijilante domin bin sahun masu garkuwar.

Ya ce duk da cewa masu garkuwa da mutanen basu tuntubi iyalansu ba, gwamnatin jihar na iya bakin kokarinta domin kubuta da mutanen.

More from this stream

Recomended