
Rikicin siyasar Togo na cikin batutuwan da suka mamaye taron
Shugabannin kasashen Kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen Afrika ta yamma, wato ECOWAS na gudanar da wani taron yini daya a Abuja.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ne ke jagorantar taron karo na 54 domin tattauna batutuwan da suka shafi yankin na yammacin Afirka.
Wasu batutuwa da taron ya mayar da hankali akai sun hada da tattauna batun samar da kudin bai-daya tsakanin kasashen yankin.
Da kuma tattauna batun rikicin siyasa a kasashen Togo da Guinea Bissau.
An dai shafe fiye da shekara daya, Togo na fama da rikicin siyasa tun watan Agustan 2017 inda masu zanga-zanga suka mamaye titunan kasar kan bukatar sauya dokar zabe.
Babu tabbas ko a taron na yau shugabannin kasashen na ECOWAS za su dauki mataki game da rikicin na Togo musamman bayan kammala zabe a ranar Alhamis.
Taron dai na zuwa duk mako daya bayan taron da aka gudanar a Abuja na shugabannin kasashen da ke kewaye da tafkin Chadi.
A wajen taron Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya da takwaransa na Chadi Idris Deby da Mahamadou Issoufou na Nijar da kuma Paul Biya na Kamaru sun amince da tsarin wasu bukatu guda takwas domin kawo karshen yaki da kungiyar Boko Haram da ta addababi yankin.