Sojoji sun kama wasu yan kunar bakin wake mata biyu

Dakarun sojan Najeriya da suka fito daga rundunar Lafiya Dole dake aikin samar da tsaro a yankin arewa maso gabas sun samu nasarar kama wasu yan kunar bakin wake mata su biyu a kauyen Mushemiri dake karamar hukumar Konduga ta jihar Borno.

Rundunar sojan ta ce yan kunar bakin wake sun shiga hannu ne lokacin da suke kokarin shiga birnin Maiduguri a ranar Laraba da daddare.

Rundunar tace an samu nasarar kwance rigar bom din da suke dauke da ita kuma ana cigaba da bincike kan lamarin.

Cikin wani sako da rundunar sojan ta wallafa a shafinta na Twitter ta bayyana cewa lamarin yafaru ne da misalin karfe 09:30 na dare.

A lokuta da dama yan kungiyar ta Boko Haram na kai hare-haren kunar bakin wake ta hanyar yin amfani da mata masu karancin shekaru koma manyan mata.

More from this stream

Recomended