Tsohon shugaban jam’iyar PDP, Ahmad Mu’azu ya gana da Osibanjo

Toshon gwamnan jihar Bauchi wanda har ila yau ya taba riƙe muƙamin shugaban jam’iyar PDP na kasa, Ahmad Adamu Muazu ya gana da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo.

Ganawar ta mutanen biyu ta gudana ne a ofishin mataimakin shugaban kasar dake fadar Aso Rock.

Muazu ya isa bangaren ofishin mataimakin shugaban yan sa’o’i kaɗan bayan da Osinbajo ya raka shugaba Buhari zauren majalisar kasa domin gabatar da kasafin kudin shekarar 2019.

Wata majiya dake fadar shugaban kasa ta ce ganawar ta mutanen biyu bata rasa nasaba da shirye-shiryen da Muazu yake na komawa jam’iyar APC.

Wata majiyar kuma ta bayyana cewa tsohon gwamnan ya ziyarci fadar ne domin ya godewa mataimakin shugaban kasar bisa halartar bikin yarsa da yayi wanda aka yi a Bauchi.

Da yan jaridar dake fadar shugaban kasa suka tunkare shi domin ya yi jawabi, Mu’azu yaki yadda ya ce komai kan abinda suka tattauna.

More from this stream

Recomended