Buhari ya sha ihu a majalisa ya yin gabatar da kasafin kudi

Wasu daga cikin yan majalisar kasa sun yi wa shugaban kasa, Muhammad Buhari ihu lokacin da yake jawabin kasafin kudi a zauren majalisar.

Ihun na yan majalisar ya sa shugaban kasar tsayawa a lokuta da dama lokacin da yake tsaka da gabatar da jawabin kasafin kudin.

Wasu daga cikin yan majalisar sun zargi Buhari da bayar da alkaluma na karya.

Dai-dai lokacin da shugaban kasar ya ce tattalin arziki da kuma sha’anin tsaro sun inganta a zamanin gwamnatinsa wasu daga cikin yan majalisar sun rika ihun “Karya! Karya.”

Ya yin da magoya bayan shugaban kasar suka riƙa tafi da sowa na nuna goyon baya,muryar ihun masu adawa da shi ta kauraye majalisar.

Shugaban majalisar dattawa, Abubakar Bukola Saraki da kuma kakakin majalisar wakilai,Yakubu Dogara sun tsaya kallo ya yin da yan majalisar suke cigaba da ihun.

More from this stream

Recomended