Ofishin hukumar zaben Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo da ke Kinshasa babban birnin kasar ya kama da wuta kwana goma kafin babban zaben kasar.
Babu cikakken bayani kan ko kayayyakin zabe sun kone.
Hukumar zaben ta ce tana aiki tukuru wurin gano abin da ya yi sanadin gobarar da kuma irin barnar da ta yi, tana mai cewa za a ci gaba da shirye-shiryen gudanar da zaben.
Warin hayakin gobarar ya mamaye birnin.
An fuskanci tashin hankali daban-daban gabanin zaben.
A kwanakin baya-bayan nan, an yi ta-ho-mu-gama da ‘yan sanda a wuraren taron siyasa – mutane da dama sun jikkata sannan an ba da rahoton mutuwar wasu.
‘Yan takara na jam’iyyun hamayya da dama sun yi kira a gudanar da bincike kan abin da ya haddasa gobarar, suna masu nuna fargaba kan yiwuwar dage zaben idan an lalata kayan zabe.
Mai magana da yawun babban dan hamayya da aka hana tsayawa takarar shugaban kasa Moïse Katumbi ya wallafa hoto a shafinsa na Twitter da ke nuna yadda gobarar ke ci, inda ya yi tambaya “shin gobarar ta Allah da annabi ce ko kuwa wasu mutane ne ke yi wa hukumar zaben zagon-kasa.”