Solomon Dalung ya ce Farfesa Ango ya ji da jikikokinsa

Gwamnatin APC ta Muhammadu Buhari ta mayar wa da kungiyar dattawan arewa da martani, inda ta ce su kama girmansu.

A farkon mako ne shugaban kungiyar dattawan arewa ta Nother Elders Forum Farfesa Ango Abdullahi ya yi kira ga mutanen yankin da kada su sake zaben Buhari saboda babu wani abin ci gaba da gawamnatinsa ta yi kusan shekaru hudu na mulkinsa.

Yayin da yake mayar da martani a hirarsa da BBC, ministan wasanni da matasa Barista Solomon Dalung ya ce ba irin wadannan kalaman ba ne suke bukata daga wajen dattawan ba.

“Ubangiji ya hana su karfin fada yanzu, ya bar su da basira ta bayar da shawarwari da kuma dora mu a kan hanya,” in ji Dalung.

Ya kara da cewa Farfesa Ango Abudllahi, matsayin uba yake a wajensa kuma dattijo ne mai martaba kwarai a arewa wanda ba zai tsaya yana ce ce ku ce da shi ba.

“Farfesa Ango yana da jikoki, sun masa yawa saboda haka bai ma san abin da ke faruwa ba a arewa. Wannan kuskure da suka ce sun gani mu ba mu gan shi ba.”

Ya ce kila ya dade Farfesan bai fita waje ba balle ya san halin da arewa take ciki.

“Duk wanda ya ce Buhari bai tabuka komi ba to bai ma shi adalci ba.”

Farfesa Abdullahi Ango shugaban kungiyar dattawan arewa
Farfesa Ango a cikin bayaninsa ya ce “Buhari ya gaza wajen magance talauci da matsalar ilimi a arewacn Najeriya,”

Ya ce arewacin Najeriya ne dandalin talauci, kuma yankin ne ya dage wajen ganin Buhari ya lashe zaben shugaban kasa a 2015.

“Mun sa ran za a samu canji bayan Buhari ya ci zabe amma mun zuba ido ba mu ga komi ba,” in ji Farfesan.

Amma a cewar minista Dalung, Buhari ya bayar da kwangilar gyaran hanyar Abuja zuwa Kano, gyaran da ya ce “PDP da ta yi shekara 16 ta manta da shi.

More from this stream

Recomended