
Sojojin Najeriya da suka fito daga runduna ta daya dake aiki a atisayen Operation Whirl Punch sun samu nasarar kama wasu rikakkun masu safarar bindigogi.
Mutanen da aka kama sun hada da Aminu Umar mai shekaru 32, Shehu Sama’ila mai shekaru 25 da kuma Bilyaminu Abdullahi mai shekaru 22.
Mutanen uku sun fada hannun jami’an tsaro a jihar Niger lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa garin Bena dake karamar hukumar Danko Wasagu ta jihar Kebbi wacce tayi iyaka da Zamfara.
A wata sanarwa da mataimakin daraktan hulda da jama’a na rundunar ,Kanal Muhammad Dole ya fitar ta bayyana cewa an kama mutanen ne a wani shingen bincike dake kauyen Rijau a jihar Niger.
Sojojin sun kwace bindigogi 44 kirar gida da kwansunan harsashi 351 dake cikin wata mota kirar Toyota Corolla mai rijistar namba ZUR 28 DX Kebbi.
A cewar sanarwar,” binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa masu safarar bindigar na kan hanyarsu ta zuwa garin Bena dake karamar hukumar Danko/Wasagu a jihar Kebbi wacce ke makotaka da jihar Zamfara.”