
Wani mutum a jihar Niger da ake kira da suna Yakubu Chanji mai shekaru 70 dan yan kai ya auri wata yarinya yar shekara 15.
Jaridar Daily Nigerian ta gano cewa daurin auren ya gudana ranar Litinin kuma ya samu halartar yan’uwa da abokan arziki.
Chanji wanda har ila yau ake kiransa da suna Nafsi-Nafsi ya samu lakanin sunan “Chanji”saboda al’adarsa ta auri saki.
“Yana kyauta sosai a yankin Kwangila dake Minna.Ya bada gudummawa sosai ga mazauna yankin musamman wajen gina musu masallaci.
“Muna kiransa Chanji saboda yana canza mata akai-akai. A iya sanina ya yi aure sama da sau 12 amma wasu mutane sun ce za iya kai wa sau 20 .
“Abin da muka sani shine a koda yaushe yana ajiye mata hudu a gidansa da zarar ya saki daya ko kuma daya ta mutu yana gaggawar maye gurbinta.”a cewar wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta.