
Ministan harkokin wajen kasar Saudiyya Adel al-Jubeir ya yi watsi da bukatar Turkiyya na mika ma ta wadanda ake zargi da kisan dan jarida Jamal Khashoggi.
Adel al-Jubeir ya ba za su mika ‘yan kasarsu ba.
A makon da ya gabata ne shugaba Racep Tayyep Erdogan na Turkiyya ya bukaci Saudiyya ta taso keyar wadanda ake zargi da kisan Mista Khashoggi bayan kotun turkiyya ta bayar da sammacin kamo su.
Saudiyya dai na tuhumar mutum 11 da kisan Khashoggi, a karamin ofishin jekadancin kasar da ke birnin Santanbul.
Wadanda Turkiyya ke so a mika mata sun hada da Saud al-Qahtani da Ahmad al-Asiri manyan na hannun damar Yarima mai jiran gdon saurar Saudiyya Muhammad bin Salman wadanda Turkiyya ke zargi da hannu da a kisan dan jaridar
Mista Jubeir ya soki gwamnatin Turkiyya kan yadda ta ke bada bayanai, tare da dagewa tana bukatar lalle a gabatar da dukkan shaidun da za su tabbatar da zargin da ake yi wa Yarima Muhammad bin Salman yana da hannu a kisan.