
Gabatar da kasafin kudin shekarar 2019 a majalisa, wani batu ne da ‘yan Najeriya ke jiran gani kafin babban zabe a kasar.
Mika wa ‘yan majalisar dokokin kasar kudurin kasafin kudin domin su tanatance a kan lokaci da kuma aiwatar da shi kamar yadda aka tsara wani babban kalubale ne da ake fuskanta kusan duk shekara a Najeriya.
Amma har yanzu bangaren zartarwa bai gabatar da kasafin kudin ba a gaban majalisa, domin fara nazari har a kai ga amince wa da shi yayin da ya rage watanni a gudanar da babban zabe a kasar.
Sai dai mai taimakawa shugaban Najeriya kan ayyukan majalisar wakilai Hon Kawu Sumaila ya ce jinkirin da aka samu ba wata matsala ba ce domin a cewarsa, wa’adin kasafin kudin 2018 bai kare ba har sai an yi sabon kasafi.
Ya ce tun tuni aka gabatar da kasafin ga majalisar ministoci wadanda kuma suka duba suka yi gyare-gyare. “Abin da kawai ya rage yanzu a aika wa majalisa ita kuma ta tsayar da ranar da za a gabatar da kasafin,” in ji shi.
Ya kara da cewa sun gabatar da kwarya-kwaryar tsare-tsare na yadda za a kashe kudi na takaitaccen lokaci a gaban majalisun tarayya kuma suna nan suna aiki a akai.
Duk da bai bayyana lokacin da za a gabatar da kasafin ba a majalisa amma ya ce nan da dan lokaci ne shugaba Buhari zai aika wa majalisa don ta ba shi lokacin da zai zo ya gabatar.
Wa za a dora wa laifin jinkirin?
Ana ganin dai babban zabe da ke tafe a Najeriya zai iya haifar da jinkiri ga lokacin gabatarwa da kuma amincewa da kasafin kudin.
Rashin mika kasafin da wuri kafin lokacin zabe zai iya sa a fita batunsa har sai an kammala zabukan gama-gari da za a yi a Najeriya daga watan Fabrairu.
Kammala aikin nazari kan kasafin kudin daga bangaren majalisa babban kalubale yayin da hankulan ‘yan siyasar zai karkata ga yakin neman zabe.
Amma Hon Sumaila ya ce maganar bin doka ya kamata a yi la’akari da ita ba jinkiri ba.
“Za mu aiki a kan lokaci daga bangaren zartarwa, kuma za mu tabbatar da mu yi aiki bisa bin doka,” in ji shi.
Ya kara da cewa za su tabbatar da kasafin kudin bai fita daga ka’idar da ake bukata ba.