Mafarauta sunyi tayin taimakawa a yaki masu garkuwa da mutane da sauran laifuka a jihar Taraba

Ƙungiyar mafarauta sun yi tayin bada taimako domin hada karfi da karfe wajen yaki da masu garkuwa da mutane dama masu aikata sauran laifuka a yankin arewa maso gabas.

Sakataren kungiyar mafarauta ta jihar Taraba,Mallam Usman Mamadu shine ya bayyana haka a wata zantawa da yayi da jaridar Daily Trust inda ya ce kungiyar a shirye take ta taimakawa jami’an tsaro a kokarin da suke na rage yawan aikata miyagun laifuka musamman garkuwa da mutane da kuma fashi da makami.

Ya kara da cewa kungiyar tana da mambobi 15000 dake kananan hukumomi 16 na jihar kuma suna taimakawa wajen shawo kan aiyukan masu garkuwa da mutane, barayin shanu dama yan fashi da makami a yankunansu.

Sakataren sun shafe shekaru da dama suna taimakawa jami’an tsaro a jihar Taraba dama sauran jihohin yankin arewa maso gabas a yakin da suke da yan tada kayar baya da sauran masu aikata laifuka.

Mallam Usman Mamadu ya ce mambobin kungiyar sun shiga yaki da masu garkuwa da mutane a kananan hukumomin,Bali Gassol,Gashaka da Donga kuma sun kama masu garkuwa da mutane da dama da barayin shanu inda suka damka su hannun jami’an tsaro.

More from this stream

Recomended