
Wani mahaifi wanda ya ce yana bin umarnin Allah ne ya kashe yarsa mai watanni tara a garin Tse-Agberagba dake karamar hukumar Konshisha ta jihar Benue.
An gano cewa mahaifin mai suna, John Depuun ya kwace yarinyar ta karfin tuwo daga hannun mahaiyarta a ranar da zai aikata abin inda ya wuce kai tsaye ya zuwa cikin daji inda ya ce ya bayar da yarinyar a matsayin sadaukarwa ga Allah.
Mazauna garin sun bayyana cewa mutumin ya amince da aikata kisan ymdomin bin umarnin Allah kuma babu wanda ya isa ya yi allawadai da abin da ya aikata saboda diyarsa ce bata wani ba.
Wasu mazauna kauyen sun bayyana cewa mutumin cewa wata kila mutumin yana da tabin hankali.
Mai magana da yawun rundunar ƴansandan jihar,Moses Joel Yamu ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce tuni mutumin ya shiga hannun jami’an tsaro kuma ana cigaba da gudanar da bincike.