Bayan kisan sojoji 44 majalisar dattawa ta tura wakilai yankin arewa maso gabas

Majalisar dattawa a ranar Alhamis ta yanke shawarar tura wata tawagar wakilai da za su ziyarci sojojin dake yaki da yan ta’addar kungiyar Boko Haram a yankin arewa maso gabas.

Majalisar dattawan ta dauki matakin ne biyo bayan wani kudiri da mataimakin shugaban masu rinjaye ,Bala Ibn Na’Allah ya gabatar.

Shugaban majalisar dattawan, Abubakar Bukola Saraki shine yaja hankalin abokan aikinsa kan abinda ya yafaru a jihar Borno hakan yasa na Na’Allah gabatar da kudirin.

“Dukkan mu muna sane da cewa munyi asarar gwarazan sojojin Najeriya su kusan 44 a arewacin jihar Borno,”Saraki yace.

Ana ta bangaren sanata Biodun Olujimi,shugabar marasa rinjaye ta yi zargin cewa gwamnati bata bayyana ainihin abinda yake faruwa a yankin arewa maso gabas.

“Akwai abinda gwamnati bata fada mana kan mutuwar wadannan sojojin.Dole mu san abinda muke fuskanta da kuma halin da wadanda suke yaki amadadinmu ke ciki,” Olujimi tace.

An gudanar da shiru na tsawon minti guda domin girmama sojojin da suka mutu.

Majalisar dattawan ta umarci kwamitinta kan sojoji da ya kai ziyarar ta’aziya ga iyalan sojojin da suka mutu da kuma babban hafsan sojin Najeriya.

More from this stream

Recomended