Ranar Lahadi ne aka buga kugen siyasa a Najeriya inda ‘yan takara a matakin tarayya za su soma yakin neman zaben 2019 gadan-gadan.Dokokin hukumar zaben kasar, INEC, sun nuna cewa 18 ga watan Nuwamba 2018 ita ce ranar da a hukumance za a soma yakin neman zaben.Mutum 78 ne ke takarar shugaban Najeriya, sai dai masana na ganin fafatawar za ta fi yin zafi ne tsakanin Shugaba Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC da tsohon mataimakin shugaban kasar Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP. Dukansu biyu shekarunsu na haihuwa sun wuce 70.Shugaba Buhari ya ce zai nemi wa’adi na biyu na shugabancin kasar ne saboda “na kammala ayyukan da na soma.”Shugaban, wanda ya kayar da Shugaba na wancan Goodluck Jonathan a zaben 2015, ya gina takararsa ne kan abubuwa uku: wanzar da tsaro, samar da ayyuka da kyautata tattalin arzikin kasar, da kuma yakar rashawaMasana harkokin tsaro da dama irinsu Malam Kabiru Adamu sun amince cewa shugaban ya samu gagarumar nasara a fannin tsaro – musamman a yaki da kungiyar Boko Haram wacce ta kashe dubban mutane sannan ta raba miliyoyi daga gidajensu.
Atiku Abubakar ya sha alwashin samar da ayyuka sai dai wasu na zarginsa da cinhanci da rashawa, ko da yake ya musanta zargin.
Kazalika an sha caccakar Shugaba Buhari saboda gaza yin tagomashi kan inganta tattalin arzikin Najeriya, ko da yake gwamnatinsa ta sha cewa zai dauki lokaci kafin kasar ta warke daga masassarar tattalin arzikin da ta fada a ciki lokacin da ta karbi mulki, kamar yadda ministar kudi Zainab Ahmed ta jaddada a hirar ta da BBC a makon jiya.Sake gina Najeriya