Boko Haram sun kona gidaje sama da 100 a Maiduguri

Aƙalla gidaje 100 aka kona ya yin wani hari da yan ta’addar kungiyar Boko Haram suka kai kan kauyen Mamanti dake Maiduguri a jihar Borno da daren ranar Laraba.

Dagacin kauyen, Muhammad Mammanti ya bayyana cewa magidanta da yawa ne suka tsere lokacin da yan ta’addar suka kawo harin.

“Da suka zo sun ajiye kekunansu kana suka tsallake wagegen ramin da ya kewaye garin,” ya ce.

“Mazauna kauyen sun ranta a nakare lokacin da suka ji karar harbin bindiga.Mutane biyu aka jikkata ya yin da aka kashe Civilian JTF daya mai shekaru 25. Ya mutu ne dai-dai lokacin da yake kokarin cetar wasu daga cikin dabbobinsa.”

Mamanti ya kara da cewa mazauna kauyen sun yi asarar kusan dukkanin abinda suke dashi inda ya ce mayakan na kungiyar ta Boko Haram sun kone kusan kaso 80 na gidajen dake kauyen.

A wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter a ranar Alhamis rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da faruwar harin inda ta ce wasu tsirarun yan ta’adda ne suka shiga kauyen inda suka yi harbin iska don tsorata mutane kafin su shiga kona gidajen dake garin.

More from this stream

Recomended