Obasanjo da Buhari za su haɗu a wajen kaddamar da littafin Gudluck

Shugaban kasa Muhammad Buhari da kuma tsohon shugaban kasa Olusegun na daga cikin manyan bakin da ake sa ran za su halarci wurin kaddamar da littafin tarihin tsohon shugaban kasa, Gudluck Jonathan.

Littafin mai suna “My Transition Hours” ya yi karin haske kan abubuwan da suka faru a zaben shugaban kasa na 2015 da kuma wasu muhimman kudurori da tsohon shugaban kasar ya zartar a karshen mulkinsa.

An shirya taron zai gudana a Otal din Transcorp Hilton dake Abuja ranar 20 ga watan Nuwamba.

Ya yin da shugaban kasa Muhammad Buhari zai kasance babban bako a wurin shi kuwa Obasanjo shine zai kasance shugaban taron.

Ana sa ran halartar shugabannin kasashen, Guinea, Togo, Kenya, Zimbabwe, Senegal, Gambia, Niger, Mali da kuma Ivory Coast.

Tsohon shugaban kasar Ghana,John Dramani Mahama da tsofaffin shugaban kasa na mulkin soja; Yakubu Gawon, Ibrahim Badamasi Babangida da kuma Abdulsalam Abubakar duk ana sa ran za su halarci wurin taron.

Theophilus Danjuma shine babban mai kaddamarwa ya yin da tsohon babban jojin kasarnan,Alfa Umar Belgore zai kasance mai ta’alikin littafin.

More from this stream

Recomended