Wata mata ta kashe kanta, mijinta da kuma ƴaƴansu

Wata mace dake zaune tare da mijinta a Makurdi babban birnin jihar Benue ta kashe mijinta da ƴaƴanta uku kana daga bisani ta hallaka kanta.

An bayyana mijin matar da suna, Nicholas Adetsav kuma dukkaninsu suna aiki ne a karamar hukumar Makurdi.

Moses Yamu, mai magana da yawun rundunar ƴansandan ya ce matar ita ake zargi da kisan iyalan nata.

Ya ce lokacin da jami’an ƴansanda suka isa gidan sun iske mijin nata bakinsa da kumfa ya yin da sauran gawarwakin yaran suke a kasa a zube ita kuma tana rike da wuka a hannunta.

Ya mu ya kara da cewa tuni rundunar ta kaddamar da bincike domin gano musabbabin da yasa ta aikata haka.

Makotan mamatan sun sheda cewa ma’auratan suna yawan fada da juna kuma a lokuta da dama mijin nata yana ce musu kada su shiga abin da babu ruwansu.

More from this stream

Recomended