Rundunar ‘yan sandan ta ce babu gaskiya a bayanan da ke kunshe a cikin rahoton da Amnesty ta fitar, Illa wani yunkuri na karkatar da hankali kan munanan laifukan da mabiya El Zakzaky suka aikata wanda ya hada da kai wa jami’anta hari.
A ranar Laraba ne dai Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty ta fitar da rahoto kan artabun da aka yi tsakanin ‘yan shi’a da jami’an tsaro inda a ciki ta ce bincikenta ya nuna cewa amfani da karfin da ya wuce kima da sojoji da ‘yan sandan Najeriya suka yi ne ya kai ga rasa rayuka da dama.
Amma rundunar ‘yan sandan ta ce ta yi nazari sosai kafin ta mayar da martani, kuma zargin da Amnesty ta yi cewa ta ga hutunan bidiyo da ke nuna ‘yan sanda da sojoji sun tartwasa ‘yan shi’a ta hanyar bude wuta ba gaskiya ba ne.
- Amnesty ta zargi jami’an tsaro da kashe ‘yan shi’a
- Kalli yadda ‘yan Shi’a suka yi zanga-zanga a Abuja
Rundunar ‘yan sandan tace rahoton na Amnesty wani yunkuri ne na karkatar da hankali ga saba doka da munanan laifukan da mabiya Ibrahim El Zakzaky suka aikata wadanda ta ce sun kunshi kai wa jami’anta hari da kona motar ‘yan sanda a Abuja a ranar 30 ga wata tare da haifar da tashin hankali a sassan birnin.
Rundunar ‘yan sandan ta ce duk da wannan, amma hakan bai sa ta yi amfani da karfi ba kan ‘yan shi’ar amma ta yi kokarin cafke mambobin kungiyar 400 da ta kama dauke da makamai da suka hada da bom da miyagun kwayoyi.
Kungiyar Amnesty dai ta zargi jami’an tsaro da harbewa tare da raunata mabiya Shi’ar a Abuja inda ta ce mutane 45 aka kashe tsakanin asabar zuwa litinin da suka gabata tare da da raunata 122.
Amma a martanin da ta mayar rundunar ‘yan sandan ta ce babu wani rahoton rasa rai da ta samu a sassan caji ofis dinta da ke Abuja kan rikicin na ‘yan Shi’a a ranar 30 ga watan Nuwamba.
Rundunar ‘yan sandan ta danganta rahoton na Amnesty a mastayin wani zagon kasa ga bincike kan ‘yan Shi’ada kuma kokarin hukunta wadanda aka kama.