
Daya daga cikin mutanen da suka kafa jam’iyar PDP, Cif Tony Anenih ya mutu yana da shekaru 85.
Jaridar The Cable ta tabbatar da cewa dattijon ya mutu ne a birnin tarayya Abuja.
Anenih ya kasance shugaban kwamitin amintattun na jam’iyar PDP kana ya taba riƙe muƙamin minista.
Tuni dai gwamnatin jihar Edo ta fitar da wata sanarwa mai inda take taya iyalansa hakurin rashin da suka yi.
Anenih ya jingine batun shiga al’amuran siyasa a shekarar 2016.