[ad_1]
Kungiyar boko haram ta kashe wata ma’aikaciyar kungiyar agaji ta Red Cross wacce mayakan kungiyar su ka yi garkuwa da ita a watan Maris din shekarar nan.
Mayakan kungiyar sun kashe Hauwa Liman, wacce ungozoma ce, ‘yan kawanaki bayan da su ka sa wa’adin.
Kungiyar agaji ta Red Cross ta ce labarin kashe Hauwa ya daga musu hankali.
Gwamnatin Najeriya ta ce kisan ungozomar rashin imani ne.
- Buhari ya yi magana da mahaifiyar Leah Sharibu
- Red Cross: Wa’adin da Boko Haram ta bayar ya kusa cika
An yi garkuwa da Hauwa da wasu sauran ma’aikatan agaji biyu a garin Rann da ke arewacin Njaeriya.
Daya daga cikinsu ita ce Saifura Ahmed Khorsa wacce kungiyar boko haram din ta kashe a watan da ya gabata.
Har yanzu dai, akwai wata daliba ‘yar shekara 15 a hannun mayakan wadanda ke da alaka da kungiyar tada kayar baya ta IS.
Leah Sharibu na daya daga cikin ‘yan makaranta 110 da aka yi garkuwa da su a garin Dapchi da ke arewa maso gabashin Najeriya a watan fabrairun da ya gabata.