APC Ta Musanta Yi Wa Bello Turji Rajista A Zamfara

Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya reshen jihar Zamfara, ta musanta jita-jitar da ke cewa an yi wa riƙaƙƙen ɗanbindiga Bello Turji rajista a matsayin mamban jam’iyyar.

Sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar a jihar, Yusuf Idris Gusau, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa, inda ya ce wasu ɓata-gari ne suka ƙirƙiro katin jam’iyyar na bogi domin ɓata wa APC suna.

Sanarwar ta ce katin da ake yaɗa wa ɗauke da hoton Bello Turji ba sahihi ba ne, tare da jaddada cewa ba a iya yi wa kowa rajista a jam’iyyar ba tare da lambar katin ɗan ƙasa ba, alhali Turji ba shi da ita.

Yusuf Gusau ya ƙara da cewa idan aka yi duba da kyau, za a gane cewa katin bogi ne, yana mai cewa yunƙurin shafa wa jam’iyyar bakin fenti ba zai yi nasara ba.

More from this stream

Recomended