Sojoji Sun Yi Ajalin ’Yan Ta’adda Shida, Sun Ceto Yarinya A Zamfara

Sojojin Najeriya sun kashe ’yan ta’adda shida tare da ceto wata yarinya da aka sace a karamar hukumar Maradun ta Jihar Zamfara.

Aikin sojan ya gudana ne a dajin Sububu ta hannun dakarun 8 Division Garrison Strike Force karkashin Operation FANSAN YAMMA.

A wata sanarwa da jami’in yada labarai na rundunar, Kyaftin David Adewusi, ya fitar a ranar Lahadi, ya ce sojojin sun fara fafatawa da ’yan ta’addan ne a kauyen Indulumu, inda aka kashe biyu daga cikinsu tare da kwato bindigar AK-47 guda daya.

Sanarwar ta kara da cewa dakarun sun wuce zuwa kauyen Ruduno, inda suka sake cin karo da ’yan ta’adda tare da kashe karin mutum hudu. A wurin an kwato wata bindigar AK-47, harsasai 28 na 7.62mm da kuma babura biyu, wadanda sojojin suka lalata.

Haka kuma, sojojin sun ceto wata yarinya da aka sace mai suna Halira Ibrahim a yayin farmakin.

Kyaftin Adewusi ya ce dakarun sun lalata sansanonin ’yan ta’adda da wuraren ajiyarsu da ke Magaji, Galakaje, Filinga da Kukatara, lamarin da ya raunana karfin ayyukan kungiyoyin a yankin.

More from this stream

Recomended