
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya dawo gida birnin tarayya Abuja bayan ya shafe kusan mako guda a kasashen Guinea Conarkry da kuma Switzerland.
Shettima ya sauka a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe dake Abuja da ya wakilci shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu a wurin bikin rantsar da, Mamadi Doumbouya shugaban kasar Guinea da kuma jagorantar tawagar Najeriya a a wurin taron tattalin arziki na duniya da aka yi birnin Davos na kasar Switzerland da aka saba gudanarwa a kowace shekara.
Bayan saukarsa a Najeriya Shettima ya bayyana cewa Najeriya ta sake kwato matsayinta na kujerar kan gaba a tattaunawa da suka shafi tsare-tsare a matakin yankin nahiya

