
Tsohon shugaban kwamitin shugaban ƙasa kan gyaran harkokin fansho, Abdulrashid Maina ya fito daga gidan gyaran hali bayan ɗaurin shekaru takwas da aka yi masa.
Maina ya shafe shekaru a gidan yarin Kuje dake Abuja inda ya yi zaman kaso bayan da aka yanke masa hukunci.
Rahotanni sun bayyana cewa babu masaniyar lokacin da Maina ya fito daga gidan yarin sai dai wasu majiyoyi sun bayyana cewa ya shafe makonni da shaƙar iskar yanci.
A watan Nuwambar shekarar 2021 ne wata babbar kotun tarayya dake Abuja ta same shi da aikata laifin almundahanar kudade da yawansu ya kai naira biliyan 2 bayan da hukumar EFCC ta gurfanar da shi a gaban kotun.
Tun a shekarar 2019 ne EFCC ta gurfanar da shi a gaban kotun karkashin mai sharia Okon Abong inda ta tuhume shi da aikata laifuka 12.
Da yake yanke hukuncin Abang ya gamsu cewa Maina ya aikata laifin satar kuɗin da yawansu ya kai biliyan 2 mallakin yan fansho” Da yawancin su suka mutu ba tare da sun mori daɗin aikin da suka yi a shekarun baya ba,” ya ce.
Abong ya yanke masa hukuncin jumullar shekaru 61 kan laifuka 12 da ake tuhumarsa da aikatawa amma zai yi shekarun ne a tare tun daga watan Oktoban shekarar 2019.

