
Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ya gana da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ranar Alhamis a fadar Aso Rock dake Abuja.
Makinde ya isa fadar shugaban kasar ne jim kadan bayan zuwan gwamnan Filato, Caleb Mutfwang.
Jaridar The Cable ta gano cewa shugaban kasa ya gana da gwamnonin biyu a lokuta daban-daban.
Makinde wanda ɗan jam’iyyar adawa ta PDP ne a yan kwanakin nan ya fito ya bayyana cewa baya goyon takarar shugaban kasa Tinubu a zango na biyu.
Da yake amsa tambayoyin yan jaridar dake fadar shugaban kasa bayan ganawar, Makinde ya ce bashi da shirin ficewa daga jam’iyyarsa.
Ya bayyana cewa hankalinsa a kwance yake a cikin jam’iyarsa ta PDP ya kuma bayyana cewa a lokuta da dama wasu abubuwan suna tasowa a ƙasa dake buƙatar an tunkare su tare da kowane ɓangare na siyasa APC da PDP domin samarwa da kasar makoma mai kyau.
Ziyarar na zuwa ne a dai-dai lokacin da ake cigaba da samun gwamnonin jam’iyar adawa suna komawa jam’iyar APC mai mulki.

