’Yan Najeriya Sun Amince Gwamnatin APC Ta Gaza – ADC

Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta ce ’yan Najeriya sun cimma matsaya cewa gwamnatin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta gaza wajen tafiyar da mulkin ƙasar.

Mai magana da yawun jam’iyyar na ƙasa, Abdullahi, ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na tashar Channels Television.

A cewarsa, ya rataya a wuyan jam’iyyun adawa su tabbatar wa ’yan Najeriya cewa suna da ingantattun hanyoyi da dabaru da za su fi na gwamnatin da ke kan mulki.

ADC ta ce irin waɗannan matsaloli na nuna gazawar shugabanci, tare da jaddada buƙatar sauyi a tafiyar da harkokin ƙasar.

More from this stream

Recomended