Bankin Duniya Ya Hango Bunƙasar Tattalin Arzikin Najeriya A 2026 Da 2027

Bankin Duniya ya ce tattalin arzikin Najeriya na kan hanyar samun bunƙasa mafi girma cikin fiye da shekara goma da suka gabata.

A cewar bankin, ana sa ran tattalin arzikin ƙasar zai ƙaru da kashi 4.4 cikin 100 a shekarun 2026 da 2027.

An bayyana wannan hasashe ne a sabon rahoton ci gaban tattalin arzikin duniya, Global Economic Prospects, da Bankin Duniya ya fitar a ranar Talata.

Sai dai wasu masana sun ce hasashen bai yi la’akari da halin rayuwa da kuma ƙalubalen da al’ummar ƙasar ke fuskanta a halin yanzu ba.

More from this stream

Recomended