Rundunar ’yan sandan Jihar Nasarawa ta kama wasu fitattun mutane biyu da ake nema ruwa a jallo bisa zargin aikata fashi da makami a sassa daban-daban na jihar.
Mutanen da aka kama sun hada da Kabiru Isah da Monday Bulus. Jami’an sashen yaki da fashi da makami na rundunar ne suka cafke su a ranar 10 ga Janairu, 2026, bayan samun sahihin bayanan sirri.
Kakakin rundunar, SP Ramhan Nansel, ya ce an kama mutanen ne a yankin Azuba Centre da ke Lafia, inda ake zargin sun je shirya wani sabon aikin laifi. Ya bayyana cewa tuni jami’an tsaro suka sanya su cikin kulawa ta musamman kafin a kama su.
A yayin kamen, ’yan sanda sun kwato bindigar G3 guda daya ba tare da lambar tantancewa ba daga hannun wadanda ake zargin. Daga bisani, a ranar Lahadi 11 ga Janairu, 2026, an kuma sake kwato wata bindigar pump-action a wani samame na daban.
SP Nansel ya ce kamen mutanen ya samo asali ne daga aikin ’yan sanda na amfani da bayanan sirri wajen yaki da laifi.
‘Yan Sanda Sun Kama Fitattun ’Yan Fashi Biyu A Lafia, Sun Kwato Bindigogi

