Kakakin majalisar dokokin Iran, Mohammad Baqer Qalibaf, ya gargadi shugaban Amurka Donald Trump da cewa Iran za ta ɗauki matakin martani idan Amurka ta kuskura ta kai hari a ƙasar don taimaka wa masu zanga-zangar adawa da gwamnati.
Qalibaf ya bayyana hakan ne yayin zaman majalisar dokokin Iran a yau, inda ya ce ƙasarsa za ta kai hari kan sansanonin sojin Amurka da ke yankin Gabas ta Tsakiya, tare da kai farmaki kan babbar ƙawarta Isra’ila, idan Amurka ta kai hari Iran.
Wannan gargaɗi na zuwa ne bayan Shugaba Trump ya wallafa a shafinsa na sada zumunta cewa Iraniyawa na neman ’yanci, kuma Amurka a shirye take ta taimaka musu.
Rahotanni sun nuna cewa an riga an sanar da Shugaban Amurka hanyoyin zaɓin matakan da ƙasarsa za ta iya ɗauka na kai hari Iran, musamman idan aka kashe masu zanga-zangar.
A halin yanzu, bayanai daga Iran na nuna cewa jami’an tsaro sun raunata ɗaruruwan masu zanga-zanga a wani yunkuri na dakile tarzomar da ta barke cikin dare.
Iran Ta Gargadi Amurka Kan Taimaka Wa Masu Zanga-Zanga

