
Gwamnatin tarayya ware biliyan ₦6.14 a matsayin kuɗaɗen tafiye-tafiye zuwa kasashen waje da shugaban ƙasa,Bola Ahmad Tinubu zai yi a shekarar 2016.
Bayanin haka na kunshe ne cikin kunshin kasafin kudin shekarar 2026.
Har ila yau kunshin kasafin kudin ya nuna cewa an ware naira miliyan ₦873.88 a matsayin kudin da za a kashe a tafiye-tafiyen da shugaban kasar zai yi a Najeriya a cikin shekarar ta 2026 hakan yasa jumullar kudin tafiye-tafiyen a cikin gida da kuma ƙasashen ketare ya kama biliyan ₦7.01.
Shima ofishin mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima an ware masa naira biliyan 1.73 a matsayin kuɗaɗen zai kashe wajen tafiye-tafiyen cikin gida da kasashen waje.

