
Mambobin majalisar dokokin jihar Zamfara su 6 yan jam’iyar PDP sun sanar da ficewa daga jam’iyar tare da komawa jam’iyar adawa ta APC.
Yan majalisar sun kafa hujja da yin watsi tare da rashin girmama kundin tsarin mulkin kasa da majalisar dokokin jihar ke yi a matsayin daya daga cikin manyan dalilansu na barin jam’iyar tare da komawa jam’iyar APC.
Mambobin majalisar sun bayyana aniyar tasu ne a ranar Laraba a yayin wani zama da suka yi a Gusau babban birnin jihar inda suka tattauna kan rikon sakainar kashi da akewa ɓangaren majalisa a jihar.
Sun ce majalisar ta zama yar amashin shatar gwamnan jihar Dauda Lawal Dare na jam’iyar ta su ta PDP.
Yan majalisar da suka sauya shekar sun hada da Hon. Bashar Gummi mamba mai wakiltar mazabar Gummi 1l, Hon Nasiru Maru mamba mai wakiltar Maru North da Bashir Masama mamba dake wakiltar Bukukuwan.
Sauran sun hada da Hon Bashir Bello mamba mai wakiltar Bungudu West, Hon Amiru Keta mamba mai wakiltar Tsafe West da kuma Hon Mukhtar Kaura mamba mai wakiltar Kuran Namoda North.
Th

