Shugaban Ƙasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya ce tafiyarsa zuwa kujerar shugabancin ƙasa ta kasance mai cike da ƙalubale da jarabawa masu yawa, inda ya danganta nasararsa da jajircewa da kuma taimakon Allah.
Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a a yayin taron Kwamitin Zartarwa na Ƙasa karo na 15 na jam’iyyar APC da aka gudanar a Abuja. Ya tuno da mawuyacin halin da ƙasar da ‘yan Najeriya suka fuskanta gabanin babban zaɓen shekarar 2023.
Ya ce a wancan lokaci, ‘yan ƙasa sun sha wahala sakamakon matsalolin tattalin arziƙi da na zamantakewa, ciki har da ƙarancin abinci, sauya fasalin kuɗi da kuma tsananin ƙarancin man fetur, wanda ya haddasa dogayen layuka a gidajen mai.
Sai dai ya ce duk da wadannan matsaloli, Allah ne ya kawo shi wannan matsayi. Ya ce, “Allah ne ya kawo mu nan. Ni shaida ce ta ikon Allah, domin ba tare da Shi ba, da ban kasance a nan ba.”
Shugaban Ƙasar ya kuma ƙarfafa wa ‘yan Najeriya guiwa da su kasance masu haƙuri da godiya duk da ƙalubalen da ake fuskanta. Ya yi kira da a ƙarfafa haɗin kai, haƙuri da jajircewa domin kare dimokuraɗiyyar ƙasar, yana mai gargaɗi cewa dole ne a tabbatar dimokuraɗiyyar Najeriya ba ta gaza ba.
Haka kuma, Tinubu ya buƙaci shugabanni da ‘yan ƙasa su nuna tausayi da kuma bai wa kowa dama, yana jaddada cewa Allah ne ke bayar da dama da kuma yanke hukuncin wanda zai zama shugaba.
Ba don Ubangiji ba, da ban zama Shugaban Ƙasa ba—Tinubu

