DSS Ta Saki Fulani Uku Da Ta Kama, Ta Ce Ba Ta Same Su Da Laifi Ba, Ta Kuma Ba Su Diyya

Wasu mutane uku ’yan ƙabilar Fulani da hukumar tsaro ta farin kaya ta DSS ta tsare tsawon watanni sun bayyana jin daɗi da kuma ɓacin rai bayan sakin su da aka yi ranar Alhamis.

DSS ta kama su ne a watan Yunin 2024 lokacin da suke sauka daga aikin Hajji, bisa zargin cewa suna da alaka da garkuwa da mutane a arewacin ƙasar.

Sai dai a wani taron manema labarai da aka gudanar a hedikwatar hukumar da ke Abuja, DSS ta ce ta gama bincike kuma ba ta gano wata alaka ta su da laifin da ake tuhumarsu da shi ba.

Hukumar ta gabatar da waɗanda ta kama – Rabiu Alhaji Bello, Umar Ibrahim, da Bammo Jajo Sarki – duk mazauna jihar Kwara. Bayan sanar da cewa su ba su da laifi, DSS ta ce ta bai wa kowane ɗaya daga cikinsu kyautar naira miliyan ɗaya a matsayin diyya.

More from this stream

Recomended