
Yan bindiga sun yi garkuwa da wasu Sinawa biyu daga wani wuri da su ke aikin ginin hanya a jihar Kwara.
Mutanen na daga cikin ma’aikata yan kasar waje dake aikin ginin hanyar Bode Saadu-Kaiama-Kosubosu da kamfanin BUA ke gudanarwa lokacin da yan bindigar da fuskarsu ke a rufe suka isa wurin inda suka rika harbin kan me uwa da wabi.
Lamarin ya faru ne a ranar Litinin a wurin aikin dake Ejidongari a karamar hukumar Moro ta jihar.
Adekimi Ojo kwamishinan yan sandan jihar shi ne ya tabbatarwa jaridar The Cable faruwar haka a ranar Juma’a.
” Eh gaskiya ne an yi garkuwa da wurin aikin ginin titi suna aiki ne da kamfanin BUA abin da zan iya fada kenan a yanzu,” ya ce.
A yan makonnin nan dai ana cigaba da samun yawan ƙaruwar garkuwa da mutane da kuma hare-haren yan bindiga a jihar ta Kwara

