Sufeto Janar Na ‘Yan Sanda Ya Ziyarci Jihar Kebbi Bayan Sace Ƴan Mata

Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya, Kayode Egbetokun, ya kai ziyara jihar Kebbi a ranar Talata, biyo bayan sace ‘yan mata daga Makarantar Sakandire ta Gwamnati ta Mata da ke Maga.

Rahotanni sun nuna cewa Egbetokun zai gana da Gwamnan Kebbi, Nasir Idris. Daga nan zai yi jawabi ga jami’an ‘yan sanda a jihar.Rahotanni sun ce wannan na daga cikin shirinsa na ziyara.

Ziyarar ta biyo bayan taron tsaro da Sufeto Janar ya halarta a Fadar Shugaban Kasa ranar Lahadi. Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne ya jagoranci zaman. A taron, an tattauna karuwar hare-haren sace-sace a jihohin Kebbi, Niger da Kwara.

Wasu manyan jami’an tsaro da suka halarci taron sun hada da Shugaban Rundunar Soji, Janar Olufemi Oluyode; Shugaban Sojin Sama, Air Vice Marshal Kelvin Aneke; Shugaban Sojin Ruwa, Rear Admiral Idi Abbas; Shugaban Sashen Sirrin Soji, Manjo Janar E.A.P. Undiendeye; Shugaban Rundunar Sojin Kasa, Manjo Janar Waidi Shaibu; da Darakta Janar na Hukumar DSS, Tosin Ajayi.

More from this stream

Recomended