Ƴan Sanda Sun Tabbatar Da Mutuwar Direban Kwamishinan Gombe a Hatsarin Mota

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Gombe ta tabbatar da rasuwar direban tsohon Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida, Col. Abdullahi Bello (mai ritaya), wanda ya rasu sakamakon raunin da ya samu kimanin sa’o’i 24 kacal bayan wani mummunan hatsarin mota da ya yi sanadiyyar mutuwar Kwamishinan da kuma jami’in tsaronsa.

A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Asabar, Jami’in Hulda da Jama’a na ‘Yan Sanda, DSP Buhari Abdullahi, ya bayyana cewa direban ya rasu yayin da ake masa magani a wani asibiti, bayan hatsarin da ya faru ranar Alhamis a kan titin Kwami–Malam Sidi–Gombe.

Abdullahi ya ce, Col. Bello, jami’in tsaron sa Corporal Adamu Hussaini, da direban suna kan hanyarsu ta dawowa daga Maiduguri, Jihar Borno, inda Kwamishinan ya halarci taron shawarwari na yanki kan batun sassaucin makamai, sake shigar da tsofaffin mayaka cikin al’umma, kafin hatsarin ya faru.

DSP Abdullahi ya bayyana marigayan a matsayin “masu sadaukar da kai ga aikin gwamnati waɗanda suka rasu suna hidima don zaman lafiya da tsaro,” inda ya ce rasuwarsu babban rashi ne ga jihar da ƙasa baki ɗaya.

More from this stream

Recomended