Adadin Mutane Da Suka Mutu Ya Kai 57 A Gobarar Tankar Mai A Jihar Neja

Adadin mutanen da suka rasa rayukansu a gobarar tankar mai da ta afku a garin Essa, karamar hukumar Katcha ta Jihar Neja, ya kai 57.

Rahoto ya nuna cewa lamarin ya faru ne a ranar 21 ga Oktoba, 2025, lokacin da tankar mai ta jujjuya kuma ta zubar da man fetur. Wasu mazauna sun yi yunƙurin ɗebo man, wanda ya haifar da fashewa mai ƙarfi. A lokacin, an ce fiye da mutane 35 sun mutu, yayin da wasu da dama suka ji rauni mai tsanani.

A wata tattaunawa da manema labarai, Daraktan Bayani da Huldar Jama’a na Hukumar Kula da Gaggawa ta Jihar Neja (NSEMA), Dr. Ibrahim Hussaini, ya tabbatar da cewa yanzu adadin mutanen da suka mutu ya kai 57, yayin da mutane 52 ke samun kulawa a asibitoci daban-daban.

Hussaini ya kara da cewa waÉ—anda suka mutu na cikin wadanda suka ji rauni sosai guda 14.

Hussaini Isah, shugaban ofishin ayyuka na Minna na Hukumar Kula da Gaggawa ta Kasa (NEMA), ya bayyana a ranar 24 ga Oktoba, 2025, cewa mutane 46 ne suka mutu a farko, sannan wani mutum ya rasu saboda rauninsa, yayin da kimanin mutane 63 ke ci gaba da samun magani a asibitoci daban-daban.

Ya bayyana cewa mutanen da suka mutu sun haÉ—a da maza 12, mata 27, da yara 6, yayin da wadanda suka ji rauni sun haÉ—a da maza 24, mata 32, da yara 7.

More from this stream

Recomended