Gobara Ta Lalata Shago Fiye da 500 a Kasuwar Shuwaki, Kano

Hukumar Kula da Gobara ta Jihar Kano ta tabbatar da barkewar gobara mai girma da ta lalata fiye da shagunan wucin gadi 500 a Kasuwar Shuwaki dake karamar hukumar Gari ta jihar Kano.

A cewar wata sanarwa da kakakin hukumar, ACFO Saminu Yusif Abdullahi, ya fitar a ranar Alhamis, lamarin ya faru ne da misalin karfe 3:25 na yamma a ranar Laraba.

Rahoton ya ce, dakin kula da gobara ya samu kiran gaggawa daga Kwamandan Tashar Gobara ta Gari, Abdulmalik Muhammed, wanda ya sanar da su game da gobarar.

An tura ma’aikatan kashe gobara daga Tashar Gobara ta Danbatta zuwa wurin nan take.

A lokacin da suka isa, sun ga cewa shaguna kimanin 529 daga cikin shagunan wucin gadi 1,000 sun riga sun lalace gaba É—aya saboda gobarar. Yankin da lamarin ya shafa ya kai kusan kafa 3,000 da fadin kafa 2,500.

Duk da girman gobarar, ma’aikatan kashe gobara sun samu nasarar dakile ta kuma hana ta yaduwa zuwa sauran sassan kasuwar. An yi amfani da famfon ruwa daga Comm 9 a aikin kashe gobarar.

Binciken farko ya nuna cewa gobarar ta samo asali ne daga wasu mutane da suka sha giya da ke zaune a cikin kasuwar, in ji sanarwar.

More from this stream

Recomended