Mutane 24 sun mutu a gobarar tankar mai a jihar Neja

Mutane da dama ne ake fargabar sun mutu a wata gobarar tankar mai da ta faru a wajejen yankin Essa dake kan titin Agaie-Bida a karamar hukumar Katcha ta jihar Neja.

Lamarin ya jawo cunkoson ababen hawa a manyan hanyoyin yankin.

Hajiya Aishatu Saadu kwamandan shiya ta  hukumar kiyaye afkuwar hatsura ta tarayya FRSC  shiyar  jihar Neja ta tabbatar da faruwar lamarin amma kuma ba za ta iya tabbatar da yawan mutanen da abun ya rutsa da su ba.

A cewarta lamarin ya jawo cunkoson ababen hawa akan babbar hanyar dake da yawan zirga-zirgar motoci.

Sa’adu ta kara da cewa rashin kyawun hanya ya jawo tsaiko wajen kai dauki da kuma aikin ceto.

Wakilin jaridar Daily Trust ya rawaito cewa mutane sama da 40 ne suka jikkata lokacin da suke kwasar mai daga tankar.

Wasu majiyoyi sun bayyana cewa tankar ta fadi ne da misalin karfe 11:00 na safe a Essan kilomita 4 daga garin Badeggi saboda rashin kyawun titin  Essan a ranar Talata.

Mutane sun yi tururuwa ya zuwa wurin inda suka rika kwasar man har ya zuwa karfe 02:00 na rana lokacin da tankar ta yi bindiga ta kama

Shugaban hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Neja, Abdullahi Baba Arah ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce mutane 24 aka tabbatar da sun mutu a yayin da wasu 40 suka jikkata.

More from this stream

Recomended